By Ishaq Dabai
Hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC reshen jihar Bauchi, a ranar Asabar, ta ce mutane uku sun rasa rayukan su a wani mummunan hatsarin mota a karamar hukumar Darazo ta jihar.
Kwamandan rundunar Yusuf Abdullahi, wanda ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a Bauchi, ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2:40 na daren Juma’a.inda yace motar mai lambar, BAU569AA, ta yi karo da wata motar ba bisa ka’ida ba, lamarin da ya kai ga rasa ikon sarrafa motar da direban ya yi wanda ya jawo faruwar hadarin.
Abdullahi ya bayyana cewa jimillar naira 21,000 aka kwato daga inda hadarin ya faru, sannan kuma “Sunan direban Moses Kefas kuma akwai mutane hudu a cikin motar, maza uku mace daya.
“Daga cikin wadanda suka mutu akwai maza biyu da mace, tare da jikkatar namiji daya.An sanar da ni cewa su mazauna unguwar Rafin Zurfi ne a cikin garin Bauchi.
“Lamarin ya afku a kan hanyarsu ta fita daga Bauchi don yin wani karin girma lokacin da lamarin ya faru,” in ji kwamandan.
Shugaban na FRSC ya ci gaba da bayanin cewa wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata an kai su babban asibitin Darazo don duba lafiyarsu da tabbatar da su.
Ya shawarci duk masu amfani da hanya da su kasance masu sane da dokokin hanya da ƙa’idoji don gujewa haɗarin da ba dole ba wanda zai haifar da asarar rayuka.