Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutum 38 sun mutu a hatsarin kwalekwale da ya kife da wasu manoma 40 a kogin Kirfi da ke Karamar Hukumar Kirfi a jihar Bauchi.
Shugaban karamar hukumar kirfi Alhaji Bappa Danmalikin Bara, ne bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai.
Alhaji Bappa, ya ce ”Ina mika sakon ta’aziyyata ga jama’ar Kirfi da jihar Bauchi game da rashin da rashin ’yan uwanmu da suka rasu a lokacin da suke hanyar su ta zuwa gona“.
Manoman su 40 sun shiga kwalekwalen yayin da kwalekwalen ya kife dasu, mutum biyu daga cikin su ne kadai suka tsallake rijiya da baya, yayin da sauran suka nutse a cikin kogin.
Shugaban Karamar hukumar, ya kara da cewa, “Mun gano gawar mutuum biyu a hanyar garin Badara yayin da sauran ba a gano su ba zuwa yanzu, sai dai muna zargin duk sun mutu”, muna fatan Allah Ya gafarta masu.