Omoregie yana mayar da martani ne ga rufe kasuwar da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi a garin Benin, inda ya ce rufe kasuwar tabbas zai yi wani wawukeken gibi wajen kara marasa ayyukan yi a tsakanin mata da matasa, wanda ya ce hakan na iya sanyawa wadansu matan su fada Harkar karuwanci a jihar.
Solomon Omoregie, daya daga cikin masu filin da aka gina kasuwar Santana dake Sapele Road a garin Benin a ranar Juma’a, ya ce rufe kasuwar Santana ya sanya akalla mata da matasa 4, 000 za su rasa ayyukansu.
Ya kara da cewa; kasuwar wacce take da shagunna akalla 4, 000 iyalai uku ne suke da kasuwar. Wanda ya ce wadannan Iyalai din kuwa sun hada da; Omoregie, Egbon da Omorogiuwa wada ya ce suma sun gada ne daga Iyayensu.
Ya ci gaba da cewa bayan sun gada wurin ne, suka yi amfani da wurin wajen taimakon Talakawa duba da irin yanayin da suka ga al’umma sun fada.
Da yake maida martani, mai baiwa gwamnan shawara, Crusoe Osagie, ya ce gwamnati ta rufe kasuwar ne sakamakon muhallin bai kamata ya zama an bude kasuwa a wurin ba. Musamman idan aka yi duba da girman kasuwar. In ji shi.
Ya ce karamar hukumar Ikpoba Okha za ta tallafawa ‘yan kasuwar da suka sha’awar komawa kasuwar da aka ware musu a yankin. Kuma a cewarsa gwamnatin jihar za ta tallafa musu da naira dubu 50 ga kowannensu, yayin da karamar Ikpoba Okha za ta tallafa musu da naira dubu 10.
A ranar 20 ga watan Oktoba, wata gobara da tashi a kasuwar Santana din ta lashe miliyoyin dukiya tare da kona shaguna sama da 300.