Mutane hudu ne suka mutu a wasu munanan hadurra guda biyu da suka afku cikin sa’o’i uku a jihar Bauchi.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar hadurran guda biyu.
“An samu hadurra guda biyu a yau, wanda ya yi sanadin asarar rayuka hudu. Hadarin na farko ya faru ne da safe a kan hanyar Awala zuwa Gidan Mai.
Ya Kara da cewa “Sai dai jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa (MTD) na rundunar ‘yan sandan jihar ne suka gudanar da aikin ceton. Wani ya kira layin jami’an mu na 122 ya sanar da mu, amma kafin mu isa wurin ‘yan sanda sun ceto su,”
Yusuf ya ce hatsarin na farko ya hada da wata Sharon da wata mota kirar Honda Civic.
Ya ce Sharon din na kokarin kaucewa karo da motar Honda Civic ne a lokacin da ta tashi daga kan titin ta yi karo da mutum guda.
Kazalika ya ce hatsarin na biyu ya faru ne a lokacin da tawagarsa ta sintiri ke kan hanyarsu ta zuwa daurin auren diyar Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu a garin Azare.
Ya alakanta musabbabin hatsarin da gudun wuce gona da iri.
A cewarsa, “Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na safe, a kilomita 7 daga kan hanyar Misau zuwa Zadawa. Mutum daya a nan take ya mutu, yayin da su biyun suka samu munanan raunuka kuma an garzaya da su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), Azare inda a nan ne aka tabbatar da mutuwar su.”
Ya ce an ajiye gawarwakin ukun a dakin ajiye gawa na FMC da ke Azare inda za a mika su ga ‘yan uwansu domin yi musu jana’iza.
Kwamandan sashin ya nanata rokonsa da cewa yakamata direbobi su mai da hankali sosai tare da kiyaye iyakar gudu da yakamata su yi, yayin da suke tuki