Mutane hudu ne suka mutu a ranar Litinin a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Legas zuwa Ibadan.
Hatsarin motan ya afku ne a tsohuwar kofar shiga garin dake, Ogere a jihar Ogun da misalin karfe 3:22 na rana.
An ce mutane biyar ne suka jikkata a lamarin, wanda ya shafi mutane tara – maza shida, mata biyu da yaro namiji daya.
Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Ogun, Florence Okpe, ta ce: “Mutane hudu ne suka mutu a hadarin, dukkansu maza ne manya.”
Okpe ya ce wata mota kirar Toyota Sienna mai lamba KJA738ET ta kutsa cikin wata tirela ta Howo mai rijistar KMC548YD.
“Abin da ake zargin ya haddasa hatsarin ne da ya wuce kima wanda ya kai ga rasa iko daga bangaren direban motar sienna, wanda ya yi karo da babbar motar a lokacin da direban motar ke kokarin juyawa.
“An kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Victory, Ogere domin kula da lafiyarsu, yayin da aka ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawa na FOS, Ipara,” in ji Okpe.
A wani labari kuma na daban.
Buhari Ya Karbi Bakoncin Gwamnonin APC 9 A Daura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin ya karbi bakuncin wasu gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
Gwamnonin da suka kai ziyarar gaisuwar Sallah sun samu jagorancin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Progressive Governors Forum (PGF), Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi.
Wadanda suka yi tafiyar sun hada da gwamnan jihar Imo, Sen. Hope Uzodimma, gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Filato, Mista Simon Lalong, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da gwamnan jihar Filato. Gwamnan jihar Nassarawa, Engr. Abdullahi Sule, Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello.
Da yake jawabi bayan taron, Bagudu ya ce shugabancin Tinubu da Shettima zai kara dacewa duk nasarorin da aka samu cikin shekaru bakwai da suka gabata a karkashin mulkin shugaba Buhari.
Bagudu ya ce gwamnonin APC na aiki tukuru domin ganin sun lashe zaben gwamnan Osun da ke tafe.
A nasa bangaren, Uzodimma ya bayyana zabin Shettima a matsayin shawarar gamayya, inda ya ce gwamnoni 22 na jam’iyyar APC za su kai jihohi 22 a zaben 2023 mai zuwa.