An kashe mutane hudu a ranar Talata yayin da jami’an tsaro suka dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a Ebonyi babban ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar.
Yan bindigar sun kai hari a hedikwatar hukumar ta NDLEA da ke Ntezi a karamar hukumar Íshíelu a jihar da misalin karfe 2 na rana.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga hedikwatar rundunar ne ta katanga.
Amma jami’an Hukumar sun dakile masu tada kayar bayan, tare gudun Mawar da sojoji da jami’an ‘yan sanda wadanda suka garzaya wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa domin bayar da dauki.
Kakakin ‘yan sandan jihar Loveth Odah, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Abakaliki.
Ta ce jami’an tsaro sun kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar yayin da wasu suka tsere da raunuka.
“Abin takaici, an kashe daya daga cikin jami’an da majiyyaci a cibiyar Hukumar,” in ji ta.
Ta ce har yanzu jami’an tsaro na ci gaba da sintiri dazuzzukan yankin domin neman wadanda suka samu raunukan da suka tsere.
Kakakin ‘yan sandan ta kuma bayyana cewa, an kwato bindigu biyu da alburusai daga hannun maharan.
“Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da harsashi guda 140 na K2, harsashi 36 na GPMG, harsashi 30 na Ak 47, Mota Kirar SUV mai gudu 4, babura, kakin soja da na ‘yan sanda da kuma laya,” inji ta.