Wasu Mutum 4 daga Ahali guda sun mutu har lahira, biyo bayan cin abinci Mai dauke da guba da su kayi, a garin Banni dake Karamar hukumar Kaiama na jihar Kwara.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wadanda lamarin ya shafa sun hadar da wasu Yara biyu, wadanda mahaifin su daya, da kuma jikokin wani mutum biyu Mai suna Alhaji Mohammed Abubakar.
Wadan da lamarin ya shafa su ne: Umar Mohammed mai shekara 25, da Kabir Mohammed Mai shekara 18, sai jikokin Alhaji Mohammed, Wanda suka hadar da Umar da kuma Bashiru.
Mai magana da yawun rundunar tsaron farar hula da kare kaddarorin gwamnatin wato Civil Defence dake jihar, Afolabi Babawale ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya danganta mutuwar mutanan da cin abinci mai dauke da guba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Maimartaba Sarkin Lafiagi ya rasu
Balarabe ya ce, Ana zargin mamatan sun mutune, bayan wani abinci da su kaci tare a ranar Laraban, inda suka mutu dukkanin su, a asibitoci mabanbanta a ranar jiya Alhamis.
Ya ce ” mun Sami sanawar mutuwar Yara biyu na Alhaji Mohammed Abubakar dake kauyen Olori na yankin Banni, dake karamar hukumar Kwara ta Arewa. Da Kuma mutuwar Umar Mohammed mai shekara 25, da Kadir Mohammed mai shekara 18″ inji shi.
“Sun fara yin amai ne da musalin Karfe 4 na safen jiya Alhamis, inda aka gaggauta kai su babban asibiti ta Igbeti na jihar Oyo ” a cewar shi.
Ya kara da cewa, ” A asibitin ne aka yi musu gwaji, kuma tabbatar dacewa, mutanan sunci abinci ne mai dauke da guba” inji jami’in