Cutar Koronabairos na ci gaba da bazuwa a Nijeriya, inda ya zuwa hada wannan rahoto, mutum 1273 ke da cutar a Nijeriya, a yayin da 239 suka warke, sai kuma 40 suka mutu sakamakon cutar.
Gwamnatin Kano dai ta koka cewa gwamnatin Buhari ta yi watsi da su, inda ba ta ba su wani tallafi, a yayin da kuma gwamnatin tarayyar ta musanta hakan.
A wani yunkuri da gwamnatoci daban-daban ke yi wajen dakile yaduwar cutar kuwa, tuni aka sanya dokar zama a gida, inda ko a jiya gwamnatin Kaduna ta sabunta dokar zaman gidan har na tsawon kwana 30.
A Kadunan, Jami’ar Ahmadu Bello za ta jagoranci yin gwajin cutar a Zariya, bayan da NCDC suka samar da wurin gwajin cutar.
Sannan hakazalika a yau ne ake sa ran jin jawabin shugaban kasa Buhari, inda mutane suke cikin zullumin ko za a sake su ne ko za a ci gaba da garkame su a gidajensu a daidai lokacin da yunwa ke ci gaba da addabar al’umma, a lokaci guda kuma cutar na ci gaba da bazuwa.