Ma’aikatar Bada agajin gaggawa ta Kasar Ukraine ta Bayyana cewa Akalla mutane 5 ne Suka Mutu sakamakon mummunan harin da Rasha ta Kai kan Tirken gidan Talbijin din kasar dake Birnin Kyiv.
Sai dai Babu tabbacin cewa ko Tirken gidan Talbijin din ya Fadi kasa ko a’a, Amma harin yayi sanadiyar daukewar shirye-shiryen gidan talbijin din.
Kazalika kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito cewa, mutane biyar sun jikkata sanadiyar harin na Rasha.
Har’ilayau Wani Rahoto ya nuna cewa, haryanzu Tirken gidan Talbijin din Mai tsayin mita 380 ,Kimanin kafa 1,250 kenan na nan a tsaye.