Cibiyar dake dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC a ranar Litinin ta ce an sake samun mutum 242 da suke da cutar Korona, inda wannan adadin ya sanya masu cutar suka kai 4641.
NCDC ta ce an sake samun mutum 10 da suka rasa ransu sakamakon cutar, wanda hakan ya sanya adadin wadanda suka rasa ransu sun kai 150.
Sai dai NCDC din sun ce cikin awa 24 ba a samu sabuwar jiha dauke da cutar ba.
Har wala yau NCDC din sun ce adadin wadanda suka warke daga cutar a Nijeriya sun kai 902.
Sabbin wuraren da aka samu masu cutar sun hada da; Legas, 88, Kano, 64, Katsina, 49, Kaduna, 13, Ogun, 9, Gombe, 6, Adamawa, 4, FCT, 3, Ondo, Oyo, Ribas, Zamfara, Borno da Bauchi sunna da 1-1.