By Abbas Yakubu Yaura
An tabbatar da mutuwar mutum daya yayin da wasu 5 suka samu raunuka bayan da wata mota kirar Toyota Highlander ta kutsa cikin wasu shaguna da ke tashar Amje a kan titin Legas zuwa Abeokuta.
An tattaro cewa wata motar kirar jeep mai lamba BDG 654 DC da wani Akinola Sulaimon ke tukawa ta afka cikin shagunan da misalin karfe 3 na yammacin ranar Lahadi.
Rahotanni sun ce Sulaimon na kan hanyar zuwa tashar motar Kola ne daga wani wurin tattara haraji lokacin da hatsarin ya afku, wanda ya yi sanadin mutuwar wani Simisola Abedoye yayin da wasu biyar suka samu munanan raunuka.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Adekunle Ajisebutu, wanda ya tabbatar da afkuwar hatsarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Ota na jihar Ogun domin yi musu magani.
Sannan ya ce, “An ajiye gawar marigayin a dakin ajiyar gawa na wannan asibitin domin a tantance gawarwakin.
Sannan an kama direban kuma yana hannun ‘yan sanda. Ana ci gaba da kokarin kwato motar da hatsarin ya rutsa da ita.
“A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Abiodun Alabi, ya bayar da umarnin a gudanar da kwakkwaran bincike kan hadarin cikin gaggawa. Inda yace yana mai jajantawa iyalan mamacin.”