By Abbas Yakubu Yaura
An tabbatar da mutuwar mutum daya bayan da wani gini ya rufta a kan titin Freeman dake Island Legas a ranar Asabar.
An bayyana cewa ginin ya ruguje ne bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da akayi a titin Freeman, dake tsibirin Legas.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas ya tabbatar da faruwar rugujewar ginin a wani rahoto na farko mai suna, ‘Rahoton halin da ake ciki a ginin bene mai hawa hudu da ya ruguje a Layin Alayaki 4, Legas Island ranar Asabar, 21 ga watan Mayu, 2022.
Rahoton ya kara da cewa, “Hukumar ta mayar da martani game da lamarin da ya faru a sama, wanda tuni ya saba wa ka’idojin tsaro.
An ceto wasu mutane biyu da ransu a wani bene mai hawa uku da ya ruguje a kan titin Freeman da ke tsibirin Legas a ranar Asabar.
Alkaluman baya-bayan nan ya kawo adadin mutanen da aka ceto da ransu daga tarkace ginin benin.
Ginin wanda har yanzu ana kan gina shi, ya fado ne a lokacin da ake tsaka da tafka ruwan sama mai karfi.
Masu aikin ceto sun hada da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Legas (LASEMA) da kuma Hukumar kashe gobara.