By Abbas Yakubu Yaura
Ana fargabar an kashe mutum daya tare da jikkata da dama bayan wasu ‘yan daba dauke da makamai sun kai hari a gidan Soka na wani dan ta’addan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, a Ibadan dake jihar Oyo.
A cewar PUNCH, Lauyan Igboho, Yomi Aliyyu (SAN), wanda ya tabbatar da faruwar harin a wata tattaunawa ta wayar tarho, ya ce ‘yan bangan sun kai farmaki gidan dan ta’addan tare da farmakar wasu mukarrabansa inda suka bar daya daga cikin na hannun damarsa.
Aliyyu ya ce ‘yan bindigar sun kai hari gidan dan ta’addan da jami’an DSS suka kai hari a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2021.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, bai ce uffan ba kan lamarin har ya zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.
Idan dai za a iya tuna cewa jami’an DSS sun kai farmaki gidan Igboho da misalin karfe 1:34 na safiyar ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2021, biyo bayan samun rahotannin sirri da ke cewa yana tara makamai.
Rundunar ‘yan sandan sirrin ta kashe biyu daga cikin abokan maharin tare da kama wasu 12 da aka sako bayan watanni.