By Abbas Yakubu Yaura
An shiga fargabar yayin mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu da dama biyo bayan sabon rikicin da ya barke tsakanin mutanen Mbakume da Mbasombo a Ikayongo da ke karamar hukumar Gwer ta Gabas a jihar Benuwe.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito daga wani ganau da ke yankin cewa rikicin daya barke a daren Laraba ya kai ga kone gidaje da gonaki da dama a cikin al’ummar.
Shaidanun gani da ido ya ce rikicin ya kasance a kodayaushe kan rikicin gonaki ne amma babu wanda ya san abin da ya jawo rikicin baya-bayan nan, watanni da dama bayan gwamnatin jihar ta dauki matakin sasanta rikicin.
Ya ce: “Ba za a iya bayyana dalilin rikicin baya-bayan nan ba amma duk mun san cewa mutanen Mbakume da Mbasombo sun rayu tamkar makiya ne saboda rashin jituwa a kan mallakar gonaki duk da matakan da gwamnatin jihar ta dauka na magance matsalar. rikici.
“Da safiyar ranar (Alhamis) an kona wani yanki na Tse-Tsuwe, an ce an kashe mutum daya sannan kuma gidan wani jami’in dan sanda mai ritaya, mai suna Yonov Aberg da sauran amfanin gonarsa ‘yan bindigar ba su bar shi ba. ”
Da aka tuntubi shugaban karamar hukumar, Mista Terwase Ortserga, wanda ya ce baya garin ne domin gudanar da aikinsa, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya.