Akalla mutum 36 ne suka mutu yayin da wasu kusan 40 kuma suka jikkata sanadiyyar hatsarin wata motar safa a Sin wadda ta yi taho mu gama da motar dakon kaya.
Rahotanni sun bayyana cewa motar na dauke da mutum 69 akan hanyarta ta zuwa yankin gabashin Jiangsu da safiyar yau Lahadi, inda ta samu matsalar fashewar taya lokacin da take tsaka da tsala gudu bisa titi, matakin da ya kai ta ga karawa wata babbar motar dakon kaya.
Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta Sin ta bayyana cewa, mutane 9 daga cikin 39 da suka samu raunuka na cikin mawuyacin hali, yayin da raunin mutane 26 ke da sassauci.
Bisa ga kididdiga dai cikin shekarar 2015 kadai, hatsarin mota ya hallaka mutane dubu 58 a titunan kasar ta Sin.