An mutuwar mutum daya tare da kwantar da wasu 13 a asibiti sakamakon barkewar annobar cutar amai da gudawa a yankin Jen-Ardido da ke karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.
Shugaban karamar hukumar, Markus Hamidu a ranar Alhamis ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a Jalingo, babban birnin jihar.
Ya kara da cewa ana kokarin ceto duk wadanda suka kamu da cutar a asibitin. “A jiya ne aka rubuta cewa mutum daya ya mutu, wasu goma sha uku kuma suna kwance a asibiti.
“A yau, ba mu sami wani bayani game da wasu matattu ko fiye da abun da samu ba kamar yadda ma’aikatan kiwon lafiya suka yi cikakken bayani a yankin don dakile barkewar cutar.
“A gaskiya ina jajantawa wadanda abun ya shafa kuma daga yanzu ba za mu dunkule hannunmu ba a fafutukar ganin an warkar da su da kuma yankin daga cutar,” in ji Hamidu.
Ya ce har yanzu ba a gano musabbabin barkewar cutar kwalarar a yankin ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wannan dai na zuwa ne watanni uku bayan da aka samu bullar irin wannan annoba a karamar hukumar Tella ta jihar Taraba inda mutane bakwai suka mutu tare da kwantar da wasu da dama a asibiti.