Akalla mutum guda ne ya mutu yayin da wasu biyar suka jikkata bayan tawagar masu zanga-zanga sun kusa Kai Ofishin yan sanda a Nkoranza dake Arewacin kasar Ghana.
A cewar rundunar Yan sandan kasar, Yayin boren, Masu zanga-zangar sun lalata Motoci a Ofishin, inda Kuma suka saki wasu Mutum 6 da Ake Zargi a dakin ajeyi masu laifi.
Rayhaan Radiyo ta gano cewa zanga-zangar da ya gudana a jiya Talata, ya faru ne biyo bayan kashe Wani matashi Mai shekarar 28 da Yan sanda suka yi, yayin Wani samame kan wadanda ake zargin Yan fashi da makami ne a yankin.
Wani jami’in kiwon lafiya ya ce, wadanda suka Sami raunikan Harbin bindiga a arangaman suna na amsan kulawar likitoci, inda Kuma yace guda daga cikin su harsashin ya sameshi a kirji.
Da Dumi-dumi: Zanga-zanga Da Harbe Harben Bindiga Sun Hargitsa Sakatariyar Jam’iyyar APC Ta Jihar Rivers
Rikicin da harbe harben bindiga da zanga-zanga ya afku a safiyar ranar Laraba a sakatariyar jam’iyyar APC da ke kan titin Woji, GRA, Fatakwal, jihar Ribas, a lokacin tantancewar ‘yan takara.
Daruruwan ‘ya’yan jam’iyyar APC ne masu biyayya ga tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Magnus Abe, suka yi dafifi a harabar, bisa zargin sace ‘yan takarar majalisar jiha da tantance wakilan mazabu/jahar.
‘Yan jam’iyyar da suka fusata an ce sun isa sakatariyar ne da misalin karfe 6:00 na safe inda suka tarar da kofar sakatariyar a kulle da makulli.
Sai dai rikicin ya fara ne lokacin da wasu daga cikin matasan suka yi yunkurin bude kofa wanda hakan ya sa ‘yan sandan da ke cikin sakatariyar jam’iyyar suka yi harbin akan iska.
Harbin dai ya haifar da bazuwar firgici a yankin yayin da ‘yan jarida da ke watsa labaran masu zanga-zangar da kuma manema labarai suka yi ta tururuwa domin tsira da rayukansu.
Idan dai za’a iya tunawa a ranar Talata 17 ga watan Mayu JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta gargadi jama’a da cewa duk wani tashin hankali na ‘yan daba a yayin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, a jihar da aka shirya yi ranar Juma’a, ba za a amince da shi ba.
Rundunar a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jihar, DSP Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, ta ce rundunar tare da sauran jami’an tsaro a jihar sun shirya tsaf yayin gudanar da zaben fidda gwani.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A bisa la’akari da zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC mai zuwa a jihar Neja da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga watan Mayu, 2022, rundunar ‘yan sandan jihar na son sanar da jama’a da jiga-jigan jam’iyyar, cewa rundunar ‘yan sandan da sauran hukumomin tsaro a jihar sun samar da isassun matakan tsaro kafin, lokacin da kuma bayan lokacin atisayen”.
“Rundunar ta kuma yi gargadin cewa duk wanda bai da wata alaka da atisayen na zaben fidda gwani to ya nisanci wurin da za a gudanar da atisayen.
Haka nan kuma ana shawartar dukkan wakilan da su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, domin rundunar a shirye take kuma ba za ta lamunci duk wani tashin hankali da ayyukan ‘yan daba ba. “.
Comments 1