An yi zargin an kashe mutum daya a lokacin da rikici ya barke a yayin babban zaben kungiyar garin Enugwu-Agidi da ke karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra.
Basaraken al’ummar yankin, Igwe Michael Okekeuche ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Vince Onyekwulu, ya rabawa manema labarai a Awka, babban birnin jihar Anambra.
Ya ce an yi wa Anayo Nworah mai shekaru 28 dukan tsiya har lahira a lokacin da ake gudanar da zaben; wanda ya haifar da soke zaben gama gari na al’umma da aka shirya tun farko na wannan shekara.
Ya roki jama’a da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda.
Ya jaddada cewa a matsayinsa na babban jami’in tsaro na al’ummar, bayan tattaunawa da wasu masu ruwa da tsaki, ya yanke shawarar soke zaben domin a samu zaman lafiya.
Onyekwulu ya ce soke zaben na da nufin dakile tabarbarewar doka da oda, tashin hankali da rashin zaman lafiya.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya ce ’yan sandan ba su da masaniyar wani rikici a yankin da ya yi sanadin mutuwa mamban kungiyar gamayyar garin.