Mutum daya ya mutu yayin da wasu mutane uku suka samu raunuka daban-daban a wani hatsarin da ya afku a ranar Lahadin nan a mahadar Osoro da ke Ore, babban titin Ore-Benin, a karamar hukumar Odigbo ta jihar Ondo.
Daily Trust ta ruwaito cewa hatsarin ya afku ne a tsakanin wata mota kirar Toyota Land Cruiser SUV mai lamba, Legas FKJ 535 HP da wata mota kirar DAF mai lamba Legas KRD 422 XB.
Mista Sikiru Alonge, Kwamandan shiyyar hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa (FRSC) a Ore, ya tabbatar wa kamfanin dillamcin labarai na Kasa NAN hatsarin.
Karanta kuma: Ondo: Mutum 9 sun kone kurmus a wani hatsarin mota
Ya ce direban motar land cruiser SUV ya rasa inda zai yi saboda gudun da ya ke yi kuma ya bugawa motar da ke tsaye a gefen titi.
Ya ce babbar mace guda ta mutu a cikin motar land cruiser, tare da mutane uku a cikinta yayin da wasu biyu suka samu raunuka ciki har da direban babbar motar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Alonge ya ce an ajiye gawar a dakin ajiyar gawa na asibitin Opeyemi da ke Ore, yayin da wadanda suka jikkata kuma an kai su asibiti domin yi musu magani.
Shugaban hukumar ta FRSC, ya bukaci masu ababen hawa da su daina gudu da sauri domin ceton rayuka da dukiyoyi, tare da tseratar da rai don iyalansu.
A wani labarin kuma: Kotu Ta Yi Fatali Da Wata Bukatar Gwamnatin Tarayya Kan Abba Kyari
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da gwamnatin tarayya ta shigar na tasa keyar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari da aka dakatar zuwa kasar Amurka.
A hukuncin da ya yanke a ranar Litinin din nan, Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi fatali da karar da Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a ya shigar, bisa hujjar cewa bukatar ba ta cika ba.