Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP mai adawa a kasar nan Shiyar Kudu Maso Kudu Cif Dan Orbih ya ce Jam’iyyar APC ba ta da dan takarar dake da nagarta da zai iya karawa da su a babban zaben 2023.
Orbih wanda ya fadi hakan ne wa manema labarai a Benin fadar gwamnatin jihar Edo, ya yi ikirarin cewa hujja ce mai girma ta alamar rashin nasara a ce har yanzu APC ta gaza zakulo mutum guda da zai tsaya mata takara a 2023.
Shi dai Cif Obi yana tsokaci ne kan yadda ake ta yamaɗiɗin cewa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ka iya tsayawa takara karkashin inuwar Jam’iyyar ta APC a 2023.
Jam’iyyar APC ta yi ta gamuwa da sukar fushin yan Najeriya sakamakon yadda abubuwa suka rikice mata, wanda kuma ake ganin kuskure ne a sake barinta ta haura karagar mulki.
Tabarbarewar tsaro na daga cikin Jigon Matsalar da ta addabi mulkin na APC wanda ke ci gaba da sanya shakku cikin zukatan yan kasa dake anya suna iya tsira kuwa.
Cif Orbih ya ce wannan na daga cikin al’amari dake kara wa PDP kwarin gwiwar ci gaba da zawarcin manyan jigogi a kasar nan da za au taiamaka mata wajen samun nasara.