Alkalumman baya bayan nan da ma’aikatar kiyon lafiyar Jamhuriyar Nijar ta fitar sun nuna cewa yanzu haka mutane 709 ne suka kamu da cutar coronavirus a kasar.
Sanarwar da ofishin ministan kiyon lafiyar kasar ta Nijar tace daga cikin mutane 75 da aka yiwa gwaji a ranar talata, an samu mutane 8 da suka kamu da cutar ta coronavirus.
Biyu daga cikin sabbin wadanda annobar ta harba mata ne, shidda kuma maza.
Rfi Hausa ta labarto cewa; kawo yanzu dai, hukumomin lafiya a Nijar sun yiwa mutane dubu 2 da 817 gwajin cutar ta coronavirus daga cikinsu kuma an tabbatar da 709 na dauke da cutar, yayinda 403 suka warke.
A jimlace kuma mutane 31 annobar ta kashe a kasar ta Nijar.