Wani hatsari da ya rutsa da motar Toyota Corolla a ranar Litinin ya halaka mutum uku daga cikin fasinjoji shida da ke cikin motar bayan motar ta kwace daga hannun matukinta
Daily Post ta ruwaito cewa, motar tana kan hanyar zuwa Kachia ne a lokacin da a rasa yadda za ta yi, kuma ta ci karo da wani rami.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Wani Bene Ya Rufta A Garin Ibadan
Daya daga cikin fasinjojin da suka tsira, Rose Ademu ta ce hadarin ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri.
“Na hau wannan motar ne daga garejin Talevision da safiyar yau, na nufi Kachia. Bayan mun kai karamar hukumar Kajuru direban ya yi ta yin gudun wuce kima, amma kuma ya ki sauraron rokon fasinjojin.” inji ta.
A WANI LABARIN KUMA: Wani Mutum Ya Harbe Kaninsa Har Lahira, Yayin Gwajin Maganin Bingida
Wani mutum mai suna Abubakar Abubakar, ya harbe kaninsa, Yusuf Abubakar, mai shekaru 12, har lahira a lokacin da yake gwada ingancin wata sabuwar laya da aka sayo da ake tana hana harbin bindiga.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Abubakar tare da mamacin ‘ya’yan wani mafarauci ne a karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.