A lokacin da yake aike wa da Sakon sa na ta’aziyya, Sanata Uba Sani Dan majalisar dattijai mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya fitar da sanarwar a shafinsa na facebook, ya na mai cewa, “Na samu labarin mutuwar babban masoyin mu, mai son gina zaman lafiya, mai martaba da kaskantar da kai, mai girma, Hon. Arc. Barnabas Bala Bantex, rashi ne wanda ya girgiza zuqata”
H.E. Bala Bantex ya Kasan ce dan siyasa ne Mai Ilimi game da siyasar, mai tsawatar wa, Mai tawali’u da saukin kai, Mai son mutane hakika ya kasan ce Mai matukar tasiri a cikin jihar Kaduna,ya jefa rayuwarsa a cikin haɗari ya tsaya tsayin daka, domin tabbatar zaman lafiya, da kwanciyar hankali.
Ya kara da cewa “Bantex baya aya jin tsoron faɗan gaskiya. A gare shi gaskiya ta kasan ce mai tsarki. Ya ƙaunaci mutanen sa na jihar Kaduna da Najeriya abar Alfaharinmu, Ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya ga yi wa mutane aiki”. Inji Sanatan.
A matsayinsa na Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, ya kasance mai cikakken biyayya ga Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sheikh Abduljabbar ya nemi Afuwa
“Ya ba da gudumma wa matuka ga ci gaban Gwamnatin. Ya kasance a cikin sahun gaba na kokarin samar da zaman lafiya na Gwamnatin. Ya yi fice a majalisar wakilai, kuma har zuwa rasuwar sa, ana mutunta shi sosai kuma ana nemansa daga tsoffin membobin Majalisar Tarayya na da, da na yanzu”inji Uba Sani.
“Jihar Kaduna da Najeriya sun yi rashin dan dimokuradiyya na gaskiya, maginin janyar tsira, mai kawo dai-dai-to, domin cikakkun mutuni” a cewar shi.
A karshe Sanatan yace, Ina mika ta’aziyata ga Iyalan Bantex, da gwamnati, da jama’ar jihar Kaduna, kan wannan rashi, da ba za a iya magance shi ba. Inda ya Kuma ce,” H.E. Bala Bantex ya huta lafiya” inji Sanatan
Comments 1