Ministan Abuja, Malam Muhammad Bello, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar mawallafin jaridar Leadership, Sam Nda-Isaiah, inda ya ce marigayin ya bada gudummawa sosai wajen ci gaban birnin tarayya Abuja.
Minista Bello ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Abuja a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana mawallafin jaridar kuma dan siyasa a matsayin wani jigo na aiki tukuru, kishin kasa, inda ya ce mutum ne jajirtacce wanda ya yi imani da hadin kan Nijeriya.