Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Kwamared Adams Oshiomole ya bayyana cewa zai yi biyayya ga hukuncin da kotu ta yanke da kuma kwamitin Jam’iyyar APC suka yanke dangane da shugabancin jam’iyyar.
Oshiomole ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a yau a asabar a birnin tarayya Abuja.
Oshiomole ya ƙara da cewa ya amince domin yiwa jam’iyyar APC biyayya kamar yadda yake a cikin kundin jam’iyyar.
Har wa yau, Oshiomole yace zai yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari biyayya wajen amincewa da duk irin hukuncin da ya ɗauka dangane da shugabancin jam’iyyar.
Oshiomhole yace idan ba a manta ba a shekarar 2018 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemo shi domin bada tashi gudunmawa wajen ciyar da jam’iyyar gaba, kuma yace ya bawa jam’iyyar gagarumar gudummawa wajen samun nasara a zaɓen shekara ta 2019.