Na bar APC sabudda Cin Hanci da yayi yawa a cikin ta — Cewar Mai Neman Ɗan Majalisar Wakilai a Osun
Ɗan Takara a Jamiyyar APC na Dan Majalisa Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Osun Muslihudeen Adekilekun ya fita daga Jam’iyyar.
Yana neman Tikitin Takarar Tsayawa a Ƙananan Hukumomi Ede ta Arewa, da Ede ta Kudu, da Egbedore a Majalisar Wakilai ta Ƙasa a Babban Zaɓen Shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da ɗumi-ɗuminsa: Kwankwaso ya isa gidan Shekarau domin tattaunawar ƙarshe kan koma wa NNPP
Adekilekun wanda yayi jawabi ga Manema labaru a Ede a ranar Asabar, ya sanar da sabuwar Jam’iyyar da zai shiga ta NNPP.
Da yake faɗin matsayar sa na canja Jam’iyya, Adekilekun yace ya kasance yana bada gudunmawa ga cigaban Jam’iyyar tun Shekarar 2011, amma duk da haka, Shuwagabannin Jam’iyyar sun kawo wani Ɗan Takara domin yin amfani da biyayyar sa da jajircewa basu amfana mashi komai ba.
Ya bayyana cewa Jam’iyyar na gudanar da tsarin ta kamar na ƴan Ƙungiyar Asiri a Ede, APC ta Kuma kasance tana ƙara inganta cin hanci da rashawa, da Siyasar Uban gida.
Ya ƙara dacewa neman yardar ƴaƴan Jam’iyyar domin karɓar sabbin magoya baya tare da Ƙarfafar yin ba dai-dai ba, duk shine ya tattaru a Jam’iyyar.