Gwamnan Jahar Bauchi Bala Mohammed, yace gwamnatin Jahar ta biya Naira biliyan 30 daga cikin bashin da ake bin gwamnatin data wuce.
Duk da Mohammed bai bayyana bashin da ake bin jahar ba, yace bashin an tsara za’a riƙa biyan bashin akan Naira biliyan 1.2 duk wata ɗaya a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Mr Mohammed ya bayyana haka a lokacin taron zaman majalisar zartarwa a ranar Litinin a Bauchi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Ganduje ya mika takaddar Kama aikin Hukumar kula da Harkokin Majalissar Dokokin jihar
Yace gwamnatin sa ta ɗauki kuɗaɗen da take turawa ma’aikatu domin aikata wasu ayyuka.
Acewar sa kuɗaɗen harajin da ake tattarawa na jahar, ya ƙaru da kashi ɗari 300 a ƙarƙashin mulkin sa.
Gwamnan yace kashi goma daga cikin kuɗaɗen harajin da ake tattarawa, an rarraba su a ƙananan hukumomi 20, domin inganta tattalin arzikin al’umma daga tushe.
Mohammed yace Gwamnatin sa na aiki tuƙuru wajen ganin tayi aiki da hukumomin tsaro domin hana ƴan ta’adda shigowa jahar.