Wani Matashi a Najeriya ya shiga halin dimuwa da tunanin irin abinda busrwarsa ke yi bayan da ya ware madaran kudi ya bude mata shagon POS.
Matashin mai suna Ikhuoria a shafin Tuwita ko kuma Born Gifted kamar yadda sunan nashi ya bayyana, ya ce budurwar tasa ta jefa shi a kwana inda take amfani da shagon POS din tame daukar nauyin karatun wani saurayin.
Ikhuoria ya shaida cewa ya bude mata shagon ne ganin irin halin rayuwa da ake ciki wanda kowa na rayuwa ne hannu baka hannu kwarya, to amma duk da haka ba ta mishi rana ba.
Ko da yake ya ce da ma shi ma yana da wata sana’a da yake yi wacce ta hada da kasuwanci, amma ya yi hakan ne don gudun bani-bani daga budurwar tasa.
Ya kara da cewa bai taɓa sanin cewa tana daukar nauyin karatun daya saurayin ba sai bayan da ta zo gidan shi tana wanka, nan ne ya fahimci hala bayan da ya dauki wayarta yana duba akwatin sako.
Duk da cewa ya yarda da ita matuka, amma a wancan lokaci kamar yadda ya bayyana sai da ya shiga kaulani, domin lokacin da ya tambayeta ta nuna mishi cewa tsohon saurayi ne ba wai suna tare ba ne.
Sai dai duk da wannan cin amana, Born Gifted ya gaza rabuwa da ita sakamakon irin kauna da yake nuna mata.