Ɗan shekara 44 Terhemen Anongo wanda aka kora daga Jami’ar Ibadan yana aji biyar a ɓangaren nazarin aikin Likitanci, yace ya cire mazantakar shi duk jini daya biyo baya, jim ƙaɗan bayan aikata lamarin, ya yi saurin zuwa Asibiti.
Dayake jawabi akan dalilan da suka sanya ya ɗauki wannan matakin cire Mazantakar shi, yace “kasan yadda sha’awa take musamman idan baka da mata, tare da bin ƙa’idojin addini. Ni ina cikin masu ruƙo da addini kuma na karanta tarihin Origen Adamantius, wani Babban Malamin coci a Egypt, Wanda ya cire Mazantakar shi don kada sha’awa ta dame shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojoji Sun Musanta Zargi Da Hannun Su A Rikicin Hako Zinare Ba Bisa Ka’ida Ba
Dayake jawabi da gidan Jaridar PUNCH a ranar Lahadi, Anongo yace ya ɗauki matakin cire Mazantakar shi sabudda addinin shi.
Yace “na cire ne saboda addini na. Amma na gayawa abokina kada ya gaya maku (ƴan jarida) saboda bana Son in matsa maku, kuma bana Son Al’umma su sani, amma sai da ya gaya maku.
A lokacin da aka buƙaci jin ranar da ya cire Mazantakar shi, ya bayyana cewar, ” na cire a ranar Litinin. Naji zafi amma na cire da sauƙi.