By Abbas Yakubu Yaura
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina yace ya daina zuwa reshen wata coci dake Abuja saboda a koda yaushe faston yana kai hari ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Adesina ya bayyana hakan ne a wata kasida a ranar Alhamis mai taken, ‘Wannan Kumuyi ya bambanta da kowa’, wanda ya rubuta a matsayin goyon bayan wata sanarwa da babban Sufeto na ma’aikata, Fasto William Kumuyi ya rubuta.
Ko da yake Adesina bai bayyana wace cocin ya daina zuwa ba, amma bayanan daya wallafa a bainar jama’a sun bayyana cewa shi mamba ne a cocin Foursquare Gospel inda aka nada shi Fasto kuma ya halarta tun a shekarar 1988.
A cikin rubun nasa mai magana da yawun shugaban kasar yace abin takaici ne yadda wasu fastoci suka mayar da minbarin su zuwa akwatunan sabulu inda suke tofa albarkacin bakinsu.
Ya rubuta cewa, “Na kasance ina halartar wani coci a Abuja daga shekarar 2015 zuwa 2018, har faston ya fara ganin kansa a matsayin wanda dole ne ya durkusar da gwamnatin Buhari, Lahadi bayan Lahadi, duk wani zargi ne daga kan mimbari. Amma na jure, tun da reshe ne na coci da na halarta fiye da shekara 30 na ina hidima, Har wata rana, na wuce gona da iri.
Mataimakin shugaban kasar, ya yaba wa Kumuyi da yace a makon daya gabata cewa kada kiristoci su “ raina masu rike da madafun iko saboda suna ganin ba sa cika alkawuran zabe”.