Wata budurwa ta nuna takaicin ta, na yadda ta taimakawa wani saurayin ta, da kudin zuwa kasar waje, amma ya dawo yaki auran ta.
Acewar budurwar wadda bata bukaci a bayyana sunan ta ba, tace ita ta dauki nauyin tafiyar saurayin ta zuwa kasar waje, amma kawai ya dawo ya biyata Naira Miliyan 50, tare da gaya mata cewa ta nemi wani saurayin, shi bazai iya auranta ba, domin tayi mashi tsufa, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaita
Ga yadda labarin ta yake:
“Ina jin yadda wasu mazaje ke yin amfani da mata, su kuma guje su, bayan sun samu duk abunda suke so, amma ta faru dani, na kasance cikin mamaki, domin gani nake kamar bazai faru ba?
Akwai wani saurayi na, dana dauki nauyin karatun sa zuwa kasar waje, shekaru da suka wuce, ya dawo, amma wannan lamari abun tunawa ne ga dukkanin iyalan mu dani kaina.
KARANTA WANNNAN LABARIN: Ni Bafillatani ne, kuma Kaka na Babban shehin malamin musulunci ne — inji Femi Fani-Kayode
Abun mamaki bayan na dauki kudaden dana ajiye na dauki nauyin tafiyar sa na tsawon Shekaru sama da 7, abun bakin ciki, bayan ya dawo, ya gayaman cewa shi bashi da ra’ayin cigaba da tarayya dani, sabudda wani dalili dashi kadai ya sanshi.
Obiora dani, mun dade muna soyayya na sama da shekaru 10, tun kafin yabar Nigeria, ni ke kula da bukatun sa, domin yana aiki da wani sanannen kamfani na sufuri dake yankin kudu masu maso gabas, kuma bashi da wani albashi mai yawa, saboda shine d’a na farko da iyayen sa suka haifa, to yana da aikace-aikace da dama, kuma ina taimaka masa a matsayi na na budurwar sa.
Kuma ina saida kayayyakin abinci, saboda soyayyar dana ke yi ma Obiora ya sanya nake taimaka masa, na dauki nauyin tafiyar sa zuwa kasar waje da tunanin idan ya dawo zamu yi aure, a dalilin alkawarin da yayi mani.
Bayan jira na tsawon Shekaru 7 ya dawo daga kasar waje, kuma ya samo kudade masu yawa, kafin ya dawo ya sayi gidaje guda biyu, daya a Lagos, daya a yankin Kudu maso gabas, eanda ya saya domin iyalanshi. Ya kuma gina guda domin iyayen sa.
Tunda ya dawo muke zuwa daga wannan otel zuwa wannan, da wuraren hole wa, yanzu wata biyu kenan, amma baiyi man maganar aure ba, ko kuma zuwa domin ganin iyaye na, watan Afrilu mai zuwa shekaru na 34.
Bayan nayi mashi magana akan haka, sai Obiora ya bani cekin kudi na Naira Miliyan 50, dana tambaye shi wadannan makudan kudade, sai yace diyya ce ya biyani, ta soyayyar da muka yi na tsawon Shekaru 10. Kuma ya bude bakin sa yace bazai iya aure na ba sabudda na tsufa, Kuma Yana bukatar mace karama, sabon jini wadda zata kula dashi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Obasanjo: Ta’addanci ne ku tara wa ƴan baya bashi
Yanzu haka, tsawon sati guda kenan bana yiwa kowa magana, dukkanin wadannan shekaru dana dade Ina jira ya zama na banza, duk mane ma na dana kora da jiran zai aure ni, to ta Ina zan fara, wa zanyiwa bayanin cewa, nayi amfani da kudade na, na dauki nauyin tafiyar sa zuwa kasar waje, Mai makon
Dan uwana. Ya dawo ya jefar dani. Abun da ciwo