Wata mata ta bayyana tarin ƙalubalen da ta fuskanta kashi-kashi, kafin ta samu daga ƙarshe ta kammala karatun ta daga jami’a.
Matar wacce a yanzu ta kammala digirinta, ta bayyana cewa sai da tayi aure har ta rabu da mijinta duk tana cikin makaranta, yayin da ta ke kula yaron ta wanda yanzu har ya kai shekara hudu a duniya, cewar rahoton Legit.ng
KU KARANTA KUMA: PDP Ta Bukaci A Kakaba Takunkumin Kasa Da Kasa da Haramtawa Buhari Yin Tafiye-Tafiye
Ta kuma bayyana cewa a lokacin karatun digirin ta mai wa’adin shekara huɗu, sai da ta gamu yajin aiki sau biyu, annoba ɗaya da baƙin ciki har sau biyu, sa sauran wasu abubuwan kuma.
Mutane da dama a soshiyal midiya da suka sharhi akan labarin ta a manhajar TikTok, sun ta ya ta murnar samun kammala karatun digirin ta, inda suka nuna cewa lallai ita ɗin jajirtacciyar mace ce.
Har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoton, bidiyon na ta ya samu sama da ‘likes’ dubu bakwai (7000), da sharhi sama da dubu huɗu (4000) a TikTok.
Bidiyon Baturiya Tana Tarairayar Mijinta Dan Najeriya, Ya Bar Mutane Baki Bude
A wani labarin na daban kuma, wata baturiya ta ciri tuta wajen tarairayar mijinta ɗan Najeriya.
Wani bidiyon wata baturiya tana ba mijinta ɗan Najeriya abinci a duƙe, ya sanya mutane da dama sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi.
Baturiyar a cikin bidiyon da aka sanya a TikTok, an nuna ta ɗauke da tire cike da. abincin sa, sannan ta durƙusa kan guiwoyinta yayin da ta ɗora abincin kan teburi a gaban mijinta