Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta jajirce wajen ganin ta kawo karshen matsalar rashin tsaro da dukkanin wani na’u’in ayyukan bata gari da ta’addanci a Nijeriya.
Buhari ya bayyana hakan ne a garin Addis Ababa na kasar Habasha a jiya a wani zama da ya yi da ‘yan Nijeriya mazauna kasar Habasha da kuma shugabar hukumar lura da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje Abike Dabiri-Erewa.
A yayin da Buhari ke jawabi an yi shirun minti guda domin jajantawa ga ‘yan Nijeriya da ‘yan ta’adda suka kashe a ranar Litinin a jihar Borno. Inda Buhari ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su bai wa hukumomin tsaro goyon baya wajen hadin kan kasar.