Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi matukar jijjiga da mutuwar Tolulope Artile matukiyar helikwaftan yaki ta farko a Nijeriya.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da Kakakinsa, Femi Adesina ya fitar, inda ya ce shugaba Buhari ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan Tolulope Artile wadda ya ce samun irinta a kasa ba karamin ci gaba ba ne ga bangare tsaro da zaman lafiya.
Har wala yau a cikin sanarwar, shugaba Buhari ya jinjina wa Tolulope saboda yadda take da kwazo a filin yaƙi domin kare kasarta daga ‘yan ta’adda, inda ya ce ba za a taba manta irin gudummawar da ta bayar ba wajen ganin zaman lafiya ya samu.