An kama wata matashiya mai shekara 21 dake aiki a wani gida da zargin lalata yaron mai gidan dake da shekara goma a duniya.
Matashiyar mai suna Anele Mathe an dauke ta aikin kula da yaron ne amma kuma ta zarce da wannan aika-aika.
Kamar yadda rahotannin kotu suka bayyana, Anele ta kutsa dakin yaron ne da talatainin dare yayin da yake barci, inda kashe duk wata wuta dake dakin gabannin afka mishi.
Bisa rahotannin da muka samu, matashiyar ta shiga dakin ne daga ita sai rigar barci inda ta tilasta wa yaron yin amfani da ita.
Sai dai majiyoyi da dama sun bayyana cewa an hana Anele gabatar da duk wata shaida gaban kuliya a wani mataki na yin belin kanta.