Wata mata da ta yi aure ba da daɗewa ba ta bayyana irin halin da take ciki da mijinta.
Da take bayyana hakan ta cikin wani shiri na gidan talabijin mai suna ‘Na ce abin da na ce’, ta bayyana yadda ta manta ta shaidawa mijinta cewa tana da miliyoyi a asusunta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ta Kashe Sama Da Naira 100,000 A Labulen Ɗakin Da Ta Kama Haya
A cewarta, mahaifinta ya ba ta kyautar kuɗi bayan aurenta wanda ya kasance al’ada a gidansu kuma mijin nata ya san wannan al’adar amma bai san ainihin adadin abinda aka bata ba.
Ta yi ikirarin cewa ta sanya kuɗin ne a cikin wani hannun jari wanda kuma Allah yasawa abin albarka har kuɗin ya hauhawa, har adadin kuɗin ya kai Naira miliyan 35 kuma ta manta ta shaida wannan maganar ga mijinta.
Ta bayyana cewa mijinta a ƙarshe ya gano kuma ya nuna rashin jin daɗinsa da ita saboda ta san halin da yake ciki kuma tana da damar taimakonsa kan halin da yake ciki na rashi amma ba ta taimaka masa ba, duk da cewar tare da ita suka kashe kuɗin na sa.
Matar ta yi ikirarin cewa ta manta da gaske kuma ba ta ga dalilin sanar da mijinta ba.
Ta Nemi Kotu Ta Raba Auranta Da Mijinta Domin Ta Auri Sabon Saurayin Da Suka Haɗu A Facebook
A WANI LABARIN KUMA:
Wata mata dake birnin Livingstone na kasar Zambiya ta saki mijinta da suka shafe shekara 11 bayan ya amince da yin lalata da wata mata da ya haɗu da ita a shafin Facebook.
Prudence Wachama, wacce ta bayyana dangantakarta da mijinta, Presco Lilayi, a matsayin na kanne da ’yar’uwa, ta ce ya ɗauke ta tamkar baiwa a gidanta.
Ta kai karar sa ne a kotun dake Livingstone Local Court A3, inda kotun ta ce ma’auratan sun yi aure a shekarar 2010 kuma Lilayi ya biya K4,500 a matsayin sadaki.