Korarren Shugaban Hukumar Kula da ƙorafe-ƙorafen Al’umma ta Jahar Kano Muhuyi Magaji Rimingado ya shiga Jam’iyyar PDP.
Dayake zantawa da Jaridar Daily Trust a ranar Lahadi, yace ya shiga jam’iyyar hamayya sabudda rashin iya siyasa da ake yi a Kano, kamar yadda ya zarga.
Rimin Gado duk da bai sanya a ranshi cewa zaiyi takara ba a shekarar 2023, yace yana cigaba da neman shawarwari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zargi Cin Zarafi: Manchester United ta Dakatar da Greenwood Har Sai Baba Ya Gani
Yace fastocin shi da suke yawo a cikin garin Kano, yana nuna alamar cewa mutane suna sane da irin ayyukan Alkhairi da yayi a lokacin da yana Shugaban Hukumar Kula da Ƙorafe-Ƙorafe.
Rimin Gado yace mutane na da dama su tallata shi domin ya dawo ya ƙara yiwa Jahar aiki.
Akan zaɓen Jam’iyyar da yayi, Rimin Gado yace yayi amanna cewa Jam’iyyar itace tafi kowace ta jagoranci Jahar dama Ƙasa baki ɗaya daga Jam’iyyar APC.