Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya ce sabanin yadda ake zato shi da magoya bayansa a jihar Ribas ba za su bar jam’iyyar PDP ba, sai dai za su ci gaba da fafutukar tabbatar da tsarin dimokuradiyyar a cikin jam’iyar.
Channels TV ta ruwaito cewa, Gwamna Wike ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a sassan jihar wanda yawansu yakai 319 a dakin taro na Banquet na gidan gwamnati da ke Fatakwal a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Barazanar Tsaro Ta Sanya DSS Buƙatar ASUU Ta Janye Yajin Aiki
Ya ce ja da baya daga fada alama ce ta rauni. Taron dai an yi shi ne domin yi wa shugabannin jam’iyyar bayanin abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar a baya-bayan nan tare da bayyana musu shirin da Gwamnan zai yi ta tattaunawa da manema labarai gobe da karfe 10 na safe domin yin magana kan halin da jam’iyyar PDP ke ciki a kasar nan.
Wike ya ce, ya shirya tattaunawar ce, domin ya bayyana batutuwa kan bangarensa, wanda ya tabbatar da cewa gaskiya ce, da kuma fallasa munanan halayen wasu da ke alfahari da kansu a matsayin shugabannin kasa.
A cewarsa, bayan tattaunawar, za a bar ‘yan Najeriya su tantance ko har yanzu irin wadannan mutanen sun cancanci karramawar da aka yi musu. Gwamna Wike ya yi mamakin dalilin da ya sa jam’iyyar PDP da ke alkawarin hada kan Najeriya ba za ta iya hada kan jam’iyyar ba.
Gwamna Wike ya ce duk da rikicin cikin gida da ake fama da shi a matakin shugabancin jam’iyar a kasa da kuma d wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP marasa godiya a jihar Rivers, jam’iyyar za ta ci gaba da rike dukkanin mukaman da aka bata a jihar.
A halin yanzu dai jam’iyyar PDP ta mamaye dukkanin kujerun sanatoci uku, kujerun majalisar wakilai 13, kujeru 32 na majalisar jiha, Shugabannin kananan hukumomi 23 da na kansiloli 319.
A WANI LABARIN KUMA: Yanzu-Yanzu: Gwamna Tambuwal Ya Zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto a yanzu shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), inda ya karbi ragamar gudanarwar daga hannun takwaransa na jihar Ekiti Kayode Fayemi.
“Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti Dr. John Kayode Fayemi a yau a wajen taron majalisar tattalin arzikin kasa da aka gudanar a fadar Aso Rock Villa dake Abuja ya mika ragamar gudanarwar ga gwamnan jihar Sokoto. Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal,” kakakin kungiyar Abdulrazak Bello-Barkindo ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis.