Wata mata ta koma neman shawara da taimako domin a halin yanzu tana dab da rasa dukkanin kadarorin ta.
A cewar ta, ta siya kadarori a asirce waɗanda ta sanya sunan ɗan’uwanta a takardun, domin tsoron cewa mijinta zai iya sakin ta ya nemi ya kwace kadarorin.
KU KARANTA KUMA: Rikicin Sudan: Mutane Kusan 7000 Daga Kasashe Mabanbanta Ne Ke Cikin Wani Hali A Iyakar Masar
Abin takaici, matar ɗan’uwan nata sai ta ji hakan kawai sai cikin gaggawa ta nemi mijinta da ya sake ta, insda ta ke buƙatar a raba kadarorin a ba ta wani kaso dgaa ciki. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Labarin na ta wanda shafin mediagist ya sanya a Instagram na cewa:
“Ni matar aure ce mai ƴaƴa uku. Mijina yana da arziƙin sa. Ina aiki kuma ya bani cikakken ƴancin na yi duk abinda na ke so da kuɗi na.”
“Na yi tari sannan Allah ya taimake ni a ɓoye na sai kadarori da dama da suka haɗa da kayan bada haya, filaye da dama da sauran su.”
“Maganar gaskiya duk ma fi yawan kadarori na da sunan ɗan’uwana nayi amfani, saboda tsoron cewa idan mijina ya sake ni, zan tsira da kadarori na.”
“Abin takaicin shine, matar ɗan’uwa na mai ƴaƴa biyu ta nemi da ya sake ta kuma tana son ya bata rabin dukiyar sa da kadarorin sa. Inda abin ya ƙara dagulewa shine, ta san da dukkanin kadarorin da na sa sunan ɗan’uwana hada kasuwanci na.”
“Sannan kuma da gaske ta ke game da maganar sakin nan da raba kadarorin. Na yi matuƙar nadamar abinda ya sa nayi hakan, ta ya ya zan tsira da kadarori na? A taimaka min da shawara.”
Wata Matashiya Ta Bayyana Gwagwarnayar Da Ta Sha Kafin Samun Digiri
Wata mata ta bayyana tarin ƙalubalen da ta fuskanta kashi-kashi, kafin ta samu daga ƙarshe ta kammala karatun ta daga jami’a.
Matar wacce a yanzu ta kammala digirinta, ta bayyana cewa sai da tayi aure har ta rabu da mijinta duk tana cikin makaranta, yayin da ta ke kula yaron ta wanda yanzu har ya kai shekara hudu a duniya,