Wani Mamba a Kwamitin Majalisar Dattijai kan harkokin zabe Bala Ibn Na’Allah ya shawarci yan Najeriya da su matsa kaimi wa wakilan su na Majalisa kan tabbatar da gyaran fuska wa Kundin zabe na kasa.
Ibn Na’Allah wanda ke wakiltar Jihar Kebbi a majalisar Dattijan, ya mika wannan bukata ce yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja.
Ya ce ko da yake an kammala jin bahasin jama’a dangane da lamarin, to amma akwai su ma yan majalisun a nasu bangare su yi wani abu.
Wannan batu nashi na zuwa ne daidai lokacin da yan majalisun ke bayyana kin aiwatar da gyaran fuskar, domin a cewar su sai dai bayan zaben 2023.
Da ya tabo ɓangaren matsalar tsaro, Na’Allah ya ta’allaka al’amarin ga rashin gaskiya da adalci da kasar nan ta yi shura a kai.