- Rundunar Sojin sama NAF ta amince da harba ruwan bamai-bamai ga farar hula
- Rundunar ta ce ta harba ruwan bama-baman ne da tunanin yan Boko Haram ne domin wurin hanyar wucewar su ce
- NAF tace ta musanta zubo da ruwan bama-baman sakamakon rahoton data samu da farko cewa jirgin bai dauke da makamai
Bayan kin amincewa da tayi da farko, Rundunar Sojin saman Nigeria NAF a ranar Alhamis ta amincewa dacewa, wani daga cikin Jirgin yakin ta dayake yaki da yan ta’adda, abin bakin ciki ya harba ruwan bama-bamai daga sama,ga Farar hula a Jahar Yobe a ranar Laraba, tare da kashe mutane tara, a yayinda wasu da dama suka samu raunuka.
Jirgin a lokacin da yake gudanar da kai samamen a Kanama ta Kudu, ya lura da wani motsi mai kama dana Yan Boko Haram, domin dama haka yan Yan Boko Haram suke yi a duk lokacin da ya suka ga jirgin. Wannan ne ya sanya matukin jirgin ya bude wuta. Yana da amfani mu sanar da al’umma cewa wannan wuri ne da Yan Boko Haram ke cigaba da gudanar da aikace-aikacen su.
“Abin bakin ciki, rahoton daya sami hedikwatar Rundunar sojin sama, ya bayyana cewa cikin kuskure jirgin ya kashe wasu farar hula, gami da raunata wasu da dama, kuma an nada kwamitin da zaiyi bincike akan faruwar lamarin.
“Rahoton farko daya musanta aikata lamarin, ya faru ne ta dalilin rahoton dake a hannun hedikwatar Rundunar, cewa jirgin daya aikata lamarin baya dauke da bama-bamai a cikin shi dazai aikata wannan mummunan lamari.