Babban Jami’i mai kula da Kano na Hukumar lura da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), Pham. Shaba Muhammad, ya karyata wani zargi na kama tarin kwayar Tiramadol a Kano, ba kamar yadda rundunar ’yan sandan jihar ta furta ba. Babban Jami’in, ya yi wannan furuci ne a daidai lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a jihar ta Kano. Ya ce abin da aka kama ba Tiramadol ba ne, magani ne mai kama da Paracetamol, kuma ba ya daga cikin masu illa ko bugarwa, sabanin yadda Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Muhammad Wakili, wanda a ka fi sani da Singham, ya yi ikirari. “Maganin da Kwamishinan ‘Yan Sandan na Kano ya kama Diclofenac Sodium BP ne, wanda ba shi da alaka da Tiramadol , amma duk da haka da maganin ya zo gabanmu a matsyinmu na masu wannan aiki na kama gurbataccen abinci ko maganin da ba shida inganci da doka ta hana a shigo da shi ko a yi amfani da shi, yanzu haka mun aika da wannan magani zuwa dakin bincikenmu don tabbatar da ingancinsa. Amma dai kafin wannan lokaci, wannan magani da Kwamishinan ‘Yan Sanda ya yi ikirarin kamawa, ba Tiramadol ba ne, magani ne da Likitoci ke rubuta wa marasa lafiya a asibiti ga masu bukatar irin sa,” in ji shi. Shaba ya ce, tsakaninsu da Rundunar Hukumar ‘Yan Sanda da kuma Hukumar yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da kuma NAFDAC, suna aiki ne kafada da kafada kuma akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu, domin kuwa kowa na da bukatar kowa don samun nasarar aikin kowannensu. Sai dai kuma, a wannan karon Kwamishinan na ‘Yan Sandan Jihar ta Kano, ya yi gaban kansa wajen ikirarin cewa ya kama Tiramadol, alhalin ba haka ba ne, don haka ya shawarci Kwamishinan Muhammad Wakili, da ya rika tuntubar Hukumar ta NAFDAC, da sauran masu ruwa da tsaki a duk lokacin da irin wannan al’amari na magunguna ya taso, domin NAFDAC ce da makamantansu ke da ruwa da tsaki wajen tabbatar da sahihancin magani ko akasin haka, amma ba Hukumar ta ‘Yan Sanda ba. Akarshe, Shaba ya yi kira tare da jan hankali wajen tabbatar da samun rijistar Hukumar NAFDAC, ga masu magunguna da abinda ya shafi abinci, yin rijista abu ne mai sauki ba mai wahala ba, domin kuwa bayanai ne ake tattarawa a kan wanda ya nemi yin rijistar da kuma yin gwaje-gwajen lafiya ta yadda mai sarrafa abinci zai kasance ba shi da wata cuta mai yaduwa da za ta iya cutar da abubuwan da yake sarrafawa domin amfanin al’umma. A takaice dai, yin rijista da NAFDAC abu ne mai saukin gaske da zarar mutum ya cika ka’idar yin ta. Haka zalika, rahotanni sun bayyana cewa, a bangare guda shi ma Shugaban Hukumar yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi na Kanon, Dakta Abdul Ibrahim, ya koka game da yadda Kwamishinan ‘Yan Sandan ya yi wannan ikirari na kama magani a matsayin Tiramadol duk da kasancewar sa na wanda ba masanin magunguna ba. Wannan dalili ne ya sa ya shawarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Kanon da ma sauran al’umma baki daya kan cewa kowa ya tsaya a iya iliminsa da aikinsa wanda hakan ne kadai zai kawo zaman lafiya da hadin kai da kuma ci gaban kasa da al’ummarta.Babban Jami’i mai kula da Kano na Hukumar lura da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), Pham. Shaba Muhammad, ya karyata wani zargi na kama tarin kwayar Tiramadol a Kano, ba kamar yadda rundunar ’yan sandan jihar ta furta ba. Babban Jami’in, ya yi wannan furuci ne a daidai lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a jihar ta Kano. Ya ce abin da aka kama ba Tiramadol ba ne, magani ne mai kama da Paracetamol, kuma ba ya daga cikin masu illa ko bugarwa, sabanin yadda Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Muhammad Wakili, wanda a ka fi sani da Singham, ya yi ikirari. “Maganin da Kwamishinan ‘Yan Sandan na Kano ya kama Diclofenac Sodium BP ne, wanda ba shi da alaka da Tiramadol , amma duk da haka da maganin ya zo gabanmu a matsyinmu na masu wannan aiki na kama gurbataccen abinci ko maganin da ba shida inganci da doka ta hana a shigo da shi ko a yi amfani da shi, yanzu haka mun aika da wannan magani zuwa dakin bincikenmu don tabbatar da ingancinsa. Amma dai kafin wannan lokaci, wannan magani da Kwamishinan ‘Yan Sanda ya yi ikirarin kamawa, ba Tiramadol ba ne, magani ne da Likitoci ke rubuta wa marasa lafiya a asibiti ga masu bukatar irin sa,” in ji shi. Shaba ya ce, tsakaninsu da Rundunar Hukumar ‘Yan Sanda da kuma Hukumar yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da kuma NAFDAC, suna aiki ne kafada da kafada kuma akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu, domin kuwa kowa na da bukatar kowa don samun nasarar aikin kowannensu. Sai dai kuma, a wannan karon Kwamishinan na ‘Yan Sandan Jihar ta Kano, ya yi gaban kansa wajen ikirarin cewa ya kama Tiramadol, alhalin ba haka ba ne, don haka ya shawarci Kwamishinan Muhammad Wakili, da ya rika tuntubar Hukumar ta NAFDAC, da sauran masu ruwa da tsaki a duk lokacin da irin wannan al’amari na magunguna ya taso, domin NAFDAC ce da makamantansu ke da ruwa da tsaki wajen tabbatar da sahihancin magani ko akasin haka, amma ba Hukumar ta ‘Yan Sanda ba. Akarshe, Shaba ya yi kira tare da jan hankali wajen tabbatar da samun rijistar Hukumar NAFDAC, ga masu magunguna da abinda ya shafi abinci, yin rijista abu ne mai sauki ba mai wahala ba, domin kuwa bayanai ne ake tattarawa a kan wanda ya nemi yin rijistar da kuma yin gwaje-gwajen lafiya ta yadda mai sarrafa abinci zai kasance ba shi da wata cuta mai yaduwa da za ta iya cutar da abubuwan da yake sarrafawa domin amfanin al’umma. A takaice dai, yin rijista da NAFDAC abu ne mai saukin gaske da zarar mutum ya cika ka’idar yin ta. Haka zalika, rahotanni sun bayyana cewa, a bangare guda shi ma Shugaban Hukumar yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi na Kanon, Dakta Abdul Ibrahim, ya koka game da yadda Kwamishinan ‘Yan Sandan ya yi wannan ikirari na kama magani a matsayin Tiramadol duk da kasancewar sa na wanda ba masanin magunguna ba. Wannan dalili ne ya sa ya shawarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Kanon da ma sauran al’umma baki daya kan cewa kowa ya tsaya a iya iliminsa da aikinsa wanda hakan ne kadai zai kawo zaman lafiya da hadin kai da kuma ci gaban kasa da al’ummarta.