Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar Bollywood ta ƙasar Indiya wato Raveena Tandon ta yi wani batu na koyar darusa a rayuwarta tunda ta taso tun tana ƙarama harya zuwa yanzu data girma.
“Na kasance tun ina ƙarama na gamu da ƙalu-bale da dama wato ƙalubalen da babu sauƙi a wanda sunsa na jigata nasha wahala sosai, amma a haka na daure na cije na jajirce da yin haƙuri akan komai na abubuwa marasa daɗi da suke faruwa a tare dani, sannan akwai manyan ƙalu-bale a ita kanta masana’antar ta Bollywood”
Raveena ta ƙara da cewa a duniya akwai malamai sosai amma kuma ta fahimci duniya itace babbar malama domin kusan duk wanda yake cikinta zai koyi darusa da dama masu daɗi da marasa daɗi.
Jaruma Raveena dai ta fara yin fim a shekarar 1991 harya zuwa yanzu, sannan kuma ta yi aure a shakarar 2004 inda ta auri Anil Thadani sannan kuma sun haifi ‘ya’ya guda 4 a shekaru 16.
Daga ƙarshe Raveena tayi kira akan cewa rayuwa tana da ƙalu-bale da yawa sai anyi haƙuri da jajircewa acikin rayuwa nan ta duniya wadda zama tabbas zamanta sai haƙuri.