Tsohon gwamnan Kaduna Ahmed Makarfi yace nagartar Malam Ibrahim Shekarau ce zata basu tabbacin cewa zai zauna tare da su a jam’iyyar PDP a karo na biyu ya sake komawa cikinta.
Makarfi ya bayyana hakan ta cikin shirin Sunrise na gidan talabijin din Channels a safiyar Talatar nan, lokacin da yake amsa tambayar cewa yaya yake ganin kan tabbacin zamansa a jam’iyyar.
Ya kara da cewa kishin kasa ne ya sanya shi barin jam’iyyar NNPP, daidai lokacin da ya fahimci cewa magoya bayansa basuyi na’am da yadda ake tafiya da shi a jam’iyyar ba.
KARANTA ANAN: Gwamnatin Tarayya Na Shirin Ciyo Bashin Naira Tiriliyan 11 a 2023
Dangane da barinsa jam’iyyar APC kuwa yace babban dalilin da ya sanya shi barin jam’iyyar a ganin su shine yadda, ya fahimci ana mayar da shi saniyar ware kan Batutuwan da suka shafi ci gaban jihar, duk da cewa yana da shawarwari masu yawa da zasu Amfanar.
A Litinin din nan ne dai Tsohon Gwamnan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Malam Shekarau ya karbi katin shaidar zama ɗan jam’iyyar PDP yayin da yayi adabo da jam’iyyar NNPP.
Makarfi dai tsohon shugaban jam’iyyar PDP ne, ya kuma bayyana cewa samun nasarar komawar Shekarau zuwa jam’iyyar su wata nasara ce da zata taimaka wajen ganin sun murkushe APC a zaben baɗi.
A wani labarin kuma: China ta maido da Dokar Kulle a Beijing, Bayan Covid-19 ta sake dawo wa da Ƙarfin ta
Miliyoyin mutane a yankunan da ke kewaye da babban birnin kasar Sin an ba da umarnin kulle su a ranar Talata, yayin da hukumomi suka ninka kokarin da suke yi don daƙile Covid-19 gabanin babban taron jam’iyyar Kwaminis mai mulki a wannan shekara.
Kusan mutane miliyan hudu a lardin Hebei, wanda ke kewaye da birnin Beijing, an umurce su da su zauna a gida har zuwa karshen mako yayin da jami’ai ke gaggawar dakile wata karamar bullar cutar.