Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya Hasiya Aminu, daga cikin tawagar alhazan jihar Kaduna.
Ta rasu ne a cikin barcin da take yi jim kadan bayan ta dawo daga dutsen Arafat, kamar yadda makwabtanta a cikin tanti suka bayyana.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/rikicin-alummomin-adamawa-gwamna-fintiri-ya-sake-sabunta-dokar-hana-fita-a-guyuk-lamurde/
Dokta Usman Galadima, babban jami’in aiyuka kuma shugaban ma’aikatan lafiya na Najeriya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa har yanzu ba a tantance dalilin mutuwar ta ba.
Ya ce tuni aka sanar da iyalan Aminu rasuwarta kuma za a yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Hasiya Aminu itace ne mahajjaciya ta biyu da ta rasu a aikin Hajjin bana 2022.
Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi a jihar Nasarawa ita ma ta rasu a makon jiya bayan gajeriyar rashin lafiya kuma an yi jana’izarta a Makkah.
Zaman Arafa a tsawon yini ya zama wajibi ga kowane mahajjaci ya cika domin yin aikin Hajji.
Alhazan Najeriya daga cikin sama da miliyan daya da ke aikin Hajjin shekarar 2022 a Arafat.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Arafat dai ita ce wurin da Annabi Muhammad S.A.W ya gabatar da hudubarsa ta karshe ranar Juma’a kafin rasuwarsa.
(NAN)
A Wani Labarin Kuma Matsalar Tsaro: Kayi Koyi da Boris Johnson ka sauka daga Mulki — Ƴan Najeriya ga Buhari
Biyo bayan yawaitar Matsalar Tsaro a Ƙasar, wasu masu ruwa da tsaki sun jaddada cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka a matsayin Shugaban Nijeriya.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa ƴan Ta’adda sun kasance suna cigaba da gudanar da ta’addanci a Ƙasar, suna Cigaba da kawo rashin zaman lafiya ga Al’umma.
Matsalar tsaro dake cigaba da fuskantar Ƙasar a ranar Talata 5 ga watan yunin, ƴan ta’adda sun kai hari ga Manyan Gwamnati, ciki har da waɗanda ke aiki da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Ayarin Shugaban Ƙasa an kai masu hari a Katsina a ranar Talata. A cewar rahoto, guda biyu daga cikin Jami’an su an jikkata su.
Sakamakon hare-hare da Kashe-kashe da ke cigaba da wakana a Ƙasa, ya fusata wasu masu amfani da Kafafen Sadarwa na Zamani suka yi kiran a daina wani gangamin yaƙin neman zaɓe, da sauran aikace-aikacen da suka shafi Babban Zaɓen mai zuwa.
Sun bayyana fatan cewa zaɓen bazai faru ba, suna masu bada misali ga aikace-aikacen ta’addanci dake wakana a faɗin ƙasar.
Da yake jawabi, Shugaban Ƙungiyar Marubuta Kare Haƙƙin Bil’adama HURIWA Emmanuel Onwubiko yace Zaɓe dole a yi shi idan Shugaban Ƙasa yaki sauka daga Mulki.
A cewar sa “Buhari baya buƙatar a gaya mashi ya ajiye aiki, idan shi ya cancanta. Babban abinda ya kamata mutum yayi ya sauka, kuma bashi da wani magani ga kowacce matsaloli tun daga farkon Gwamnatin sa.
Haka zalika, wani Jigo a Jam’iyyar PDP wanda yayi jawabi daga Jahar Benue daya bukaci a sakaye sunan sa, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa daya amshi kiran ƴan Najeriya ya sauka daga mulki, kamar yadda Firaministan Landan Boris Johnson ya yi.
Yace “Shuwagabannin Afirka a kowane lokaci so suke su mutu suna kan mulki. Ƴan Najeriya sun daɗe suna kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka, amma har yanzu yana nan a Villa, shin wannan shine Shugaba.