NAHCON ta tantance Jirage 7 da zasu yi Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2022
Hukumar Kula da Hajji ta Najeriya (NAHCON) a ranar Litinin ta fara tantance Jiragen Sama da zasu yi Jigilar Maniyyata Aikin Hajji.
A halin Kamfanin Jiragen Sama guda bakwai suka nuna sha’awar Jigilar Maniyyata Aikin Hajji.
KARANTA WANNAN LABARIN: Anambra: Ƴan Bindiga sun kashe Sojoji 2, sun ƙona Sakatariya, Kotu, Motoci 32
Kamfanin Jiragen Saman sun haɗa da Azman, da Med-View da Max Air, sa FlyNas, da Skypower Express, da Westlink, da Arik.
Daga cikin bakwan guda 6 dukkanin su sun kasance masu Jigilar Matafiya a cikin gida, a yayinda FlyNas ya kasance Kamfanin Jirgin Saudiyya ne.
An gano cewa, shirin tantancewar zai kasance tantance takardu ne na Jiragen Masu Sha’awa, biyo bayan Kiran da NAHCON tayi.
Wata Majiya tace tuni an tantance Jiragen a Shekarar 2020 kafin su fara shirin ɗaukar Maniyyata Aikin Hajji amma aka dakatar sakamakon cutar Covid-19.
A lokacin da aka tuntuɓi Mai Magana da Yawun Hukumar Kula da Aikin Hajji Hajiya Fatima Sanda Usara ta tabbatar cewa akwai shirye-shirye na yin amfani da Jiragen da aka tantance a Shekarar 2020.
Tace an ƙaddamar da Kwamitin Tantancewar domin sake duba takardun kowane jirgi.
Comments 1