By Ishaq Dabai
Hukumar inshora ta kasa (NAICOM) na shirin aiwatar da inshorar gine gine fiye da hawa biyu, a cikin kasar.
Alhaji Sabiu Abubakar, Mataimakin Kwamishinan Inshora da fasaha shine wanda ya bayyana hakan a wani taron bita na jami’an kashe gobara, a Abuja, ranar Laraba.Yace NAICOM za ta aiwatar da tanade tanaden dokar da ta dace don amfanin jama’a.
Kalaman nasa, “Ya isa a ce yanzu zama dole a sanya matakan aiwatar da inshorar Ginin Jama’a a Najeriya.”Bugu da ƙari, bari in kawo muku tanadin sashe na 65 na Dokar Inshorar shekarar 2003 wanda ya tanadi cewa duk ginin jama’a za a sami inshorar data dace. Hakanan, Sashe na 64 na Dokar ya bada cewa duk gine ginen da ake yi sama da hawa 2 za a sami inshorar da ta dace dashi.
“Yana da kyau a lura cewa Hukumar za ta iya cimma wannan aikin da kyau tare da cikakken haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Jihohi.Taron bita na yau wani bangare ne na yunƙurin cimma nasarar aikin da aka yi kamar yadda yake kunshe cikin manyan dokoki. ”
A cewarsa,”Ya nuna matukar damuwa ga Hukumar cewa mafi yawan gine ginen jama’a da gine ginen da ake yi sama da hawa 2 ba su da isasshen inshora mai da cewa kuma abin daya dace, wanda hakan ya kara jaddada bukatar matakan gaggawa da Hukumar ta sanya don tabbatar da cewa wadannan gine -gine suna da isasshen inshora.
Alhaji Abubakar yace asalin Inshorar gine ginen jama’a da gine ginen da ake kan ginawa sama da hawa biyu shine don rage tasirin da rage nauyin ga mai shi wanda gwamnati zata ɗauka a cikin yiwuwar aukuwar bala’i kamar bala’o’i, wuta, hadari, rushewar gini, raunuka ko mutuwa ga wasu.
A jawabinta, Mista Debbie Windele, wanda ta jagoranci tawagar Hukumar kashe gobara tace kungiyarsu a shirye take ta hada kai da NAICOM don cimma burin.