Naira Biliyan 900 da aka fitar domin yaƙi da Ta’addanci bai isa ba– Lawan
Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Ahmad Lawan ya ce Naira biliyan 900 da aka amince da shi don yaƙi da rashin tsaro a kasar nan bai wadatar ba.
Lawan, yayin da yake jawabi ga ƴan Majalisar jim kaɗan gabanin ɗage zaman Majalisar Dattijai domin hutun shekara, ya koka kan yadda ƴan ta’adda ke kashe-kashe da kuma naƙasa ƴan Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jahar Nasarawa Ta Bada Umurnin Rufe Makarantu saboda rashin Tsaro
Ya ce, “Na damu musamman kamar mu a nan, ta hanyar tattaunawa da muke yi har da muhimmin zaman mu na rufe majalisar a yau.
“Dole ne mu (Gwamnatin Tarayya) mu yi taka tsantsan kuma alhakin da ya rataya a wuyanmu, musamman tabbatar da kare rayukan ƴan kasarmu.
“Halin tsaro ya kasance abu ne mai matuƙar wahala da ƙalubale, amma a ƴan kwanakin nan, an samu ƙaruwar hare-hare da kashe-kashe da naƙasa ƴan kasar.
“A matsayinmu na wannan gwamnatin, a koyaushe za mu ba da irin tallafin da sojojinmu da sauran hukumomin tsaro ke bukata.
“Mun yi hakan a baya ta hanyar kasaftawa da kuma amincewa da ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2022, inda aka ba da sama da Naira biliyan 900 a matsayin ƙarin kudade ga Hukumomin Tsaro.
Mun san cewa ba zai wadatar ba, amma hakan yana da muhimmanci, kuma muna sa ran hukumomin tsaronmu za su yi aiki fiye da yadda suke yi a halin yanzu.”
Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma sanar da ƴan majalisar cewa za a iya kiransu a lokacin hutu don halartar abubuwan da ke faruwa a ƙasar idan bukatar hakan ta taso.