Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabi kai tsaye ga al’ummar kasar nan, a gobe Asabar 1 ga watan Oktoba, na shekarar 2022.
Jawabin shugaban kasar wani bangare na bikin ranar samun yanci kai, wanda ake murnar cika shekaru 62 da samun yancin kai daga turawan Ingila.
KARANTA ANAN: Ibrahim Gusau ya zama shugaban NFF
Mashawarci na Musamman ga shugaban kasar Mr Femi Adesina ne ya sanar da hakan a wata Sanarwa da aka rabawa manema labarai a yammacin Juma’ar nan.
Sanarwa ta bayyana cewa za a jona jawabin nasa ne kai tsaye ta kafofin yada labarai na Talabijin da Radio na gwamnati, da kuma sauran wasu kafofin yada labaran.
A wani labarin kuma: 2023: Ba Mu Da Dan Takarar Shugaban Kasa, Inji Jam’iyyar ADC
Babban daraktan jam’iyyar African Democratic Congress ADC Sulieman AbdulAzeez, ya ce jam’iyyar za ta shiga zaben 2023 ba tare da dan takarar shugaban kasa ba.
Da yake magana da manema labarai a wani shiri a Kaduna ranar Juma’ar nan, ya ce an kori dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Mista Dumebi Kachukwu.
Da aka tambaye shi ko menene rikicin da ke faruwa a jam’iyyar, sai ya ce, “Ba mu kalli abin da ke faruwa a jam’iyyarmu a matsayin rikici ba, muna ganin kamar yadda ake daukar matakin ladabtarwa na al’ada ga mambobinmu, wannan kuma wani karin haske ne ga jam’iyyarmu.
Saboda muna kokarin kawo wani sabon tunani a cikin dimokuradiyyar Najeriya inda ba mu da mutanen da za su tafi ba tare da izini ba idan sun karya kowace doka.