Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya (NIHSA) ta roki hukumomi a jihohi daban-daban da su jajirce wajen ganin an kiyaue kara samun ambaliyar ruwa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Babban Daraktan hukumar NIHSA, Clement Nze, wanda ya bayar da sanarwar a wata sanarwa a ranar Juma’ar nan a Abuja, ya bukaci jihohi da su dauki matakan da suka dace don hana mummunar matsalar ambaliyar ruwa a shekaru masu zuwa.
Karanta kuma: Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Sama da 200 A Garin Makurdi
Acewarsa, Najeriya yanzu haka tana cikin kalubalan yanayi na ambaliyar ruwa, don haka akwai bukatar gwamnati musamman a matakin jihohi da na kananan hukumomi su kara kaimi tare da daukar matakan dakile bala’o’i masu alaka a yankunansu.
Nze ya bayyana cewa kusan dukkan jahohi 36 da babban birnin tarayya Abuja sun fuskanci ambaliyar, ya yi alhinin faruwar lamarin a jihar Jigawa inda mutane sama da 72 suka mutu.
Ya yi gargadin cewa tsarin kogunan Neja da Benuwai sun fara habaka kuma Najeriya tana kan iyakar kogin Neja da kasashe tara suka mamaye.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa shugaban NIHSA musamman ya roki hukumomi a jihohi 13 da suka hadu a manyan kogunan Neja da Benue da su samar da isassun matakan da suka dace don dakile duk wani bala’i da zai biyo baya.
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Kebbi, Niger, Adamawa, Taraba, Benue, Nasarawa, Kogi, Edo, Delta, Anambra, Cross River, Rivers da Bayelsa.
A wani labarin kuma: Dalilin Da Yasa Muke Kashe Makudan Kudade Wajen Gudanar Da Zabe – INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) a ranar Juma’a ta yi karin haske kan dalilin da ya sa ake kashe makudan kudade wajen gudanar da zaben.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar ta INEC ne ya yi wannan karin haske a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani taron tattaunawa da kungiyar Editoci ta Kasa (NGE) mai taken ‘The Editors’ Forum’ a Legas.